Jamus da Indiya sun tabbatar da aiki tare
May 30, 2017Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi taron manema labarai Firaminista Narendra Modi na kasar Indiya, wanda yake ziyara a kasar ta Jamus, inda kasashen biyu suka yi alkawarin aiki tare ta fannin tabbatar da ci gaba a kasashen duniya.
Tattaunawa tsakanin shugabannin biyu ta mayar da hankali kan fannonin hadin kai a bangaren fasaha, da makamashi, gami da yaki da ta'addanci. Kana kasashen na Jamus da Indiya sun saka hannu kan yarjeniyoyiy da suka kulla lokacin ziyarar ta firaministan Indiya a birnin Berlin.
Sannan Jamus ta nuna jin dadi kan yadda Indiya ta rungumi bangaren makamashi da ake sabunta mai amfani da hasken rana, wanda Jamus ta kware a kai. Jamus ta kasance babbar kawa ga Indiya cikin kasashen Tarayyar Turai, abin da ya saka wannan ziyara ta Firaminista Narendra Modi take da muhimmanci a kasar ta Jamus.