Kafofin yada labaran Jamus da Italiya sun janye daga Rasha
March 5, 2022Kafofin yada labarun kasashen Jamus da Italiya sun cimma matsayar kwashe ma'aikatansu daga Rasha, a wani mataki na kauce hatsarin da ke tattare da ci gaba da aiko da rahotanni daga can, tun bayan da majalisar dokokin Rasha ta saka doka da ta ce ana yayata labarun bogi a wannan rikici da ke kasar da Ukraine.
Kafopfin ARD da Na ZDF na Jamus da kuma RAI na kasar Italiya sun bi jerin wasu takwarorinsu da suka dakatar da ayyukansu har na zuwa wani lokaci.
Mai magana da yawun tasoshin ARD da ZDF ya ce daukar wannan mataki na da matukar muhimmanci, suma a daya bangaren kafar yada labarai mallakar kasar Italiya ta RAI ta ce za ta ci gaba da bibiyar abin da ke faruwa amma ba daga Rasha ba.
Sabuuwar dokar dai ta kunshi kwashe tsawon shekaru 15 a yari ga duk wanda aka kama da laifin yada labarai da mahukuntan na RAsha suka kira na bogi a kan rikicin da ke faruwa, kuma tuni dokar ta fara aiki.