Erdogan na ci gaba da ziyararsa a Jamus
September 28, 2018Merkel ta yi wannan batu ne yayin taron manema labarai da suka gudanar a wannan Juma'ar tare da shugaban na Turkiyya inda ta ke cewa: "Jamus nan bukatar ganin Turkiyya ta kasance mai kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki. Lalle mun kuma tattauna kan batun hulda tsakanin kasashen biyu, musamman ma ziyarar da ministocinmu suka yi kafin wannan ta shugaban Turkiyya. Ta haka ne muka dora daga inda aka tsaya. Mun tattauna kan mahimman abubuwa. Kuma nan gaba Ministan tattalin arzikin Jamus Peter Altmeier, zai je Turkiyya, inda kwamitin kasashen biyu zai yi wani babban zaman taro na tsakanin Jamus da Turkiyyan a karo na biyu."
Merkel ta kuma ce suna shirya wani babban zaman taro da za su gudanar da zai hada da shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Rasha Vladimir Putin da kuma Shugaba Erdogan na Turkiyya kan batun yankin Idlib na kasar Siriya.