Jamus: Demokradiyya ba ta fiskantar barazana
October 3, 2017Jam'iyyar ta AfD dai kawo yanzu ita ke zama jam'iyyar adawa ta uku mafi girma a majalisar dokokin Jamus.
Wolfgang Schaueble, da zai sauka daga mukamin ministan kudin na Jamus inda zai koma shugaban majalisar dokokin Jamus ya fadawa gidan jaridar Bild am Sonntag cewa, jam'iyyar AfD me kyamar baki da ke sanya kafa a majalisar a karon farko da juyayyun manufofi ba za ta iya wani tasiri da ake fargabar za ta iya ba, kasancewar wasu abubuwan da suke muradi kundin tsarin mulkin Jamus ba zai ba su dama ba.
Schaueble dan shekaru 75 daga jam'iyyar 'yan Conservative ya karbi sabon mukamin ne bisa kwarin gwiwa da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke da shi a kansa yayin da jam'iyyarsu ta sanya shirin kawance da 'yan fafutikar kare muhalli ta Greens da 'yan gaba-gaba a kare manufofin kasuwanci Free Democrats wadanda za su iya neman mukamin na ministan kudi.