Farfado da huldar Maroko da Jamus
August 30, 2022Kasar Marokodai, na da mahimmanci ga Turai da Jamus a fannonin tattalin arziki da yaki da bakin haure na Afirka da ke son zuwa Turai da ma fannin makamashi. Ba dai batun yawon bude ido da Maroko ta yi fice a kai ne kawai ya mamaye musaya tsakaninta da Jamus ba. Andreas Wenzel da ke zama shugaban cibiyar harkokin kasuwanci na Waje a Casablanca, ya ce a cikin shekaru 10 da suka gabata Maroko ta zama wata muhimmiyar kasa ta zuba jari ga kamfanonin Jamus a Afirka kuma a yanzu ita ce ma a matsayi na biyu bayan Afirka ta Kudu. Kamfanonin Jamus, sun samar da ayyukan yi kusan 40,000 a Maroko. Ko da rikicin diflomasiyya bai kawar da musayar kamfanoni masu zaman kansu tsakanin kasashen Jamus da Maroko ba, a maimakon haka ma dai shekarar 2021 ta samar da ci-gaban a fannin ciniki. Jarin da aka zuba, ya zarta darajar Euro miliyan dubu daya da miliyan 400. Amma baraka da Marokon, ta haifar da koma baya a wani yanki mai mahimmanci na Jamus. Har yanzu dai ana ta hasashen dalilan da suka haddasa rikicin tsakanin Maroko da Jamus, sai dai Maroko ta ji takaicin yadda Jamus ba ta fito fili ta nuna amincewa da yammacin Sahara a matsayin wani yanki na Moroko ba.
A halin da ake ciki dai, bangarorin biyu sun bayyana cewa suna son kawar da rashin fahimtar da ke tsakaninsu. Fadar mulki ta Berlin ta bayyana kudirin Moroko na samar da kwarya-kwaryan 'yancin cin gashin kai na yankin yammacin Sahara, a matsayin muhimmin mataki na samun mafita cikin ruwan sanyi. Ko ma ya za ta kaya dai, dangantaka ta inganta fiye da bara tsakanin kasashen biyu. Amma kasar ta Maroko ta kasance abokiyar hulda mai matsala, musamman a fannin kare hakkin dan Adam. Ana zargin ta da kulle 'yan jarida da 'yan adawa tsawon shekaru, bisa zarge-zarge marasa tushe. Sannan batun yammacin Saharar da Maroko ke mamaye da shi wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa, shi ma yana da matukar muhimmanci a dangantaka tsakanin Jamus da wannan kasa ta yankin Maghreb. Abdeljabbar Aarach malami a tsangayar shari'a da kimiyyar siyasa a jami'ar Hassan I a Setat ya ce har yanzu da sauran rina a kaba, dangane da inganta dangantaka tsakanin Jamus da Maroko. Shehin malamin siyasar ya kuma jaddada sauran bukatun tattalin arziki na bai daya, yana mai cewa da yawa daga cikin kamfanonin Jamus 150 da ke Maroko na amfani da kasar ne a matsayin gada.