Lafiya
Fargabar sake barkewar corona a Jamus
November 12, 2021Talla
Wannan bukata ta sake kakaba tsauraran dokokin yaki da cutar corona a Jamus din dai, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazanar sake barkewar cutar a karo na hudu. Cibiyar ta Robert Koch ta gabatar da shelar gaggawa ta soke manyan bukukuwa da ake shirin gudanar wa, a wani mataki na rage yaduwa cutar.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, ministan lafiyan kasar Jens Spahn ya jaddada bukatar daukar matakan gaggawa da za su dakile yaduwar coronan ko kuma kasar ta fuskanci Disamba mai daci. Cibiyar Robert Koch ta tabbatar da cewar mutane sama da 263 daga cikin dubu 100 ne ke kamuwa da cutar a kowace rana tsawon kwanaki biyar, wanda ke nufin kusan mutane dubu 50 na kamuwa da cutar a kullum.