1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Jamus: Fargabar karancin ruwan sama

Ahmed Salisu
April 26, 2020

Kwararru a fagen hasashen yanayi a Tarayyar Jamus sun ce akwai yiwuwar fuskantar karancin ruwan sama a wannan shekara ta 2020 da muke ciki wanda hakan ka iya kaiwa ga haifar da fari.

https://p.dw.com/p/3bOgf
Deutschland | Wetter | Jahresrückblick 2019 | Trockenheit
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Meyer

Mojib Latif da ke zaman mai bincike kan yanayi a Jamus ne ya ambata hakan a wata hira da ya yi da jaridar nan ta Rhein-Neckar-Zeitung a wannan Asabar din, inda ya ce alal misali hasashen da suka yi ya nuna cewar ruwan da za a yi a makon gobe bai taka kara ya karya ba.

Baya ga matsalar fari da kamfar ruwan za ta haifar, kwararru sun ce bishiyun da ke kasar da dama za su fuskanci babban kalubale saboda karancin ruwa da za a iya fuskanta wanda hakan illa ce babba ga muhalli.

A bara ma dai an fuskanci karancin ruwan sama a Jamus, inda sassan kasar daban-daban suka fuskanci yanayin zafi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi inda zafin ya kai maki 40 a ma'aunin Celsius.