Shirin daukar matakan dakile Covid-19 a karo na biyu
July 16, 2020Talla
Daga cikin sabbin dokokin, za a hana shiga da fice daga duk yankunan da aka sami karuwar cutar. Ana sa ran cimma matsayan karshe kan wannan mataki a wannan rana ta Alhamis.
Jamus da ta sami saukin annobar idan an kwatantata da sauran makwabtanta, ba ta son cutar tai mata zuwan bazata a wannan karon wanda hakan ya sa suka yanke shawarar daukan matakai tun da wuri.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar talatar da ta gabata ta nuna goyon bayanta ga wannan mataki.