1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwajin cutar covid 19 kyauta ga masu dawo wa hutu

Binta Aliyu Zurmi
July 24, 2020

A wannan rana ta Juma'a ce Jamus ta yanke shawarar bada gwajin cutar coronavirus kyauta ga wadanda ke dawowa kasar daga hutun rani.

https://p.dw.com/p/3ftAF
Deutschland Covid-19 Test am Flughafen Frankfurt
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Jamus din ta yanke wannan shawarar ce bayan da a yan kwanakin nan ta sami karuwar masu kamuwa da cutar, wanda ke wa kasashe barazana a cewar mahukuntan na Jamus.

A wata sanarwar da ministan lafiya na kasar ya fitar Jens Spahn, ya ce yadda ake samu karuwar masu kamuwa da cutar na nuni da cewar har yanzu ana tsakiyar wannan annoba, minista Spahn ya kara da cewar a sabili da haka dole a dauki matakan da suka kamata.

Masu dawowa daga kasashen da cutar ta yi yawa za a gudanar musu da gwajin ne tun daga filin jirgin sama.

A baya dai Jamus ta yi nasarar dakile wannan cutar cikin hanzari matakin da take son dauka a yanzu domin dakile dawowar cutar a karo na biyu.