1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauye-sauyen jagororin soja a Jamus

March 14, 2023

Sabon ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya sallami babban hafsan sojojin kasar daga mukaminsa, bayan sun samu rashin fahimta kan karfin sojan Rasha da ke yaki a Ukraine.

https://p.dw.com/p/4OdQ8
60. Jubiläum des Élysée-Vertrags | Frankreich, Paris | Eberhard Zorn
Hoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

Wata majiya da ke kusa da ministan tsaron na Jamus ta ce za a maye gurbin tsohon babban hafsan sojojin kasar Janar Eberhard Zorn wanda ke rike da wannan mukami tun shekarar 2018 da Carsten Breuer shi ma janar a rundunar sojan Jamus, sai dai ba ta yi wani karin haske kan dalilan da suka sa aka cire hular janar Zorn din ba. A watan Satumbar bara dai tsohon babban hafsan sojojin na Jamus ya bayyana damuwarsa kan rashin karfin dakarun Ukraine wajen samun galaba kan Rasha, tare kuma da bayyana fargabar cewa bayan Ukraine Rashan ka iya kai farmaki a wata kasar cikin kasashen da ke zagaye da ita.