1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da hana shigo da makamashin Rasha

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 3, 2022

Ministan tattalin arziki na Jamus kana mataimakin shugaban gwamnati Robert Habeck ya nuna rashin goyon bayansa kan hana shigo da makamashi daga Rasha.

https://p.dw.com/p/47yPZ
Jamus I Rikicin Ukraine I Robert Habeck I Taron Manema Labarai
Ministan tattalin arziki kana mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Robert HabeckHoto: Annette Riedl/dpa/picture alliance

Robert Habeck ya nuna rashin goyon bayan nasa ne a wani taron manema labarai, inda ya ce matakin hana shigo da makamashin ka iya janyo matsala a Jamus din: "Ba zan goyi bayan saka takunkumi kan bangaren shigo da man fetur da iskar gas daga Rasha ba, a gaskiya ma zan yi adawa da hakan saboda in har aka hana shigo da man to zai haifar da gagrumar matsala ga al'ummar Jamus."

A cewarsa gwamnatin Jamus din na kokarin ganin ta samar da sauyi kan dogaron da ta yi da shigo da makamashin daga Rasha, sai dai har yanzu ta dogara ne da shigo da shi daga waje.