1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kamfanin Lufthansa ya saye jiragen Air Berlin

Gazali Abdou Tasawa
October 12, 2017

Babban kamfanin jiragen sama na kasar Jamus na Lufthansa ya sanar a wannan Alhamis da saye sama da kaso 50% na jiragen kishiyarsa ta Berlin Air wanda ya durkushe. 

https://p.dw.com/p/2lj1K
Deutschland Lufthansa & Air Berlin | Symbolbild Übernahme
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Kamfanin jiragen sama na kasar Jamus na Lufthansa ya sanar a wannan Alhamis da saye sama da kaso 50% na jiragen kishiyarsa ta Berlin Air wanda ya durkushe. 

Shugaban Kamfanin na Lufthansa Carsten Spohr ya ce a karkashin yarjejeniyar cinikin da suka cimma da kamfanin na Air Berlin, kamfanin ya sayi  jirage 81 daga cikin 144 da kamfanin na Air Berlin ya mallaka, kana zai dauki dubu uku daga cikin dubu takwas da 500 da ma'aikatan wannan kamfanin. 

Wannan ciniki zai kara karfafa karfin kamfanin na Lufthansa wanda da zama kamfanin jiragen sama mafi girma a kasar ta Jamus inda yake rike da kashi 34% na kasuwar jigilar jiragen sama a kasar. Carsten Spohr shugaban kamfanin na Lufthansa ya ce yanzu kamfanin Lufthansa na da kaso uku cikin dari na kasuwar jigilar pasinja a duniya kana kaso 14% na kasuwar Turai.

Ba a dai kai ga bayyana a hakumance kudin da cinikin ya tashi ba, amma dai wasu kafofin yada labarai na kasar ta Jamus sun ambato miliyan dubu da dari biya na Euro.