1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kotu ta kori karar jam'iyyar AfD

Abdullahi Tanko Bala
September 18, 2024

Kotun tsarin mulki a Jamus ta kori karar da Jam'iyyar AfD mai kyamar baki da shigar gabanta kan takaddamar shugabancin kwamitoci a majalisar dokokin tarayya ta Bundestag.

https://p.dw.com/p/4kmFM
Alkalan kotun tsarin mulki a Jamus
Hoto: Uwe Anspach/dpa/picture alliance

Kotun ta ce kwamitoci a majalisar Bundestag suna da 'yancin zabar wanda zai shugabance su sannan suna da yancin kin zabar dan takarar jam'iyyar AfD.

Alkalan kotun sun yanke hukuncin cewa jam'iyyar mai tsananin ra'ayin rikau ba ta da dama ko wajibcin shugabantar wani kwamiti duk da cewa a bisa al'ada, karfin jam'iyyar a yanzu za ta iya jagorantar wasu kwamitoci.

Kotun ta ce 'yan kwamitin shari'a a majalisar dokokin sun yi aiki bisa 'yancinsu a 2019 inda suka kada kuri'ar fidda shugaban AfD Stephan Brandner.

Da wannan hukunci, kotun ta rusa kararraki biyu da AfD ta daukaka inda ta yi da'awar cewa hana mata damar shugabantar kowane kwamiti na majalisar a yanzu zai rage mata karfin tasiri.