Bukatar hana kyamar yaki da corona
September 22, 2021Talla
Jens Sphan ya bayyana hakan ne bayan wani sabani kan sa takunkumin fuska da ya jagoranci harbe wani matashi mai shekaru 20 da ke aiki a gidan mai a karshen mako.
Ministan na lafiya ya ce bayan kwashe tsawon watanni 18 da kasar ta yi tana fama da annobar corona, kuncin halin da mutane suka shiga kar ya kaisu ga daukar doka a hannuwansu.
Sphan ya ce kisan gillar da aka yi wa matashin na zuwa ne a daidai lokacin da yaduwar kin jinin al'umma ke karuwa ta kafafen sada zumunta.
Batun kuma da ke zuwa gabanin gudanar da zaben 'yan majalisar wakilan kasa a fadin Jamus, wadda za ta jagoranci samar da sabon shugaban gwamati da zai maye kujerar Angela Merkel a bangaren jam'iyyar da ta samu rinjaye.