Jamus: Ma'aikatan filayen jiragen sama za su tafi yajin aiki
January 30, 2024Ma'aikatan da ke aiki a sashen tsaro na manyan filayen jiragen saman Jamus za su tsunduma yajin aikin gama-gari domin neman karin albashi, inda wannan mataki ke kasancewa a fannin tattalin arziki na sufurin jiragen sama a nahiyar Turai.
Kungiyar ma'aikatan ta Verdi ta sanar da cewa mambobinta za su kauracewa aiki a filin zirga-zirgar jiragen sama mafi girma a Jamus da ke Frankfurt da kuma na Berlin babban birnin kasar har ma da wasu filayen jiragen sama guda tara a sassa dabam-dabam na Jamus din.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce har yanzu ba a samu daidaito ba wajen fitar da matsaya kan karin albashi da hukumomin filayen jiragen saman Jamus, amma abin da suke bukata shi ne karin euro biyu da centi 80 kwatankwacin dalar Amurka uku a duk sa'a guda tare da samar da sauran kayan aikin da za su rage wa ma'aikatan radadin hauhawar farashi da ake fuskanta a kasar.