Jamus: Mahawara kan kawancan CDU da SPD
January 22, 2018Ana cigaba da samun ra'ayoyi mabanbanta tsakanin 'yan siyasa da Jamusawa bayan da jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi kuma babbar ta adawa watau SPD ta sha da kyar wajen cimma amincewa da shiga tattaunawar kafa gwamnatin hadaka a hukumance da Shugabar Gwamnati Angela Merkel.
A wani lokaci nan gaba ne a yau shugaban jam'iyyar SPD Martin Schulz zai gana da Angela Merkel da shugaban jam'iyyarta ta CSU a yankin Bavaria Horst Seehofer, domin nazarin yadda za su kafa tubalin tattaunawar, gabanin kaddamar da tattaunawar a hukumance a ranar gobe Talata.
SPD na muradin ganin an samu ingantuwa dangane da batutuwa da cimma yarjejeniya a kai da jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiyan, a wani yunkuri na neman amincewar 'yan jam'iyyar da ke dari-dari da yunkurin shiga gwamnatin hadakar. Hilde Mattheis 'yar majalisar SPD ce....
"Ta ce abu guda ne muke ta jeka ka dawo a kai tun daga ranar 24 ga watan Satumba. Muna muradin ganin makomar wannan jam'yya. Wajibi ne mu san inda aka ajiye matsayinmu. A irin wannan gagarumar hadaka, rasa makomar jam'iyyarka kake, ba ka nasara".
SPD din dai na neman cimma daidaito da jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta shugabar gwamnati Merkel a kan batutuwa muhimman da suka hada da 'yan gudun hijira da sashin kiwon lafiya. Kashi 56 na wakilan jam'iyyar ne dai suka kada kuri'ar amincewa da kaddamar da tattaunawar yiwuwar kafa gwamnatin hadakar, a taron kasa da SPD ta gudanar a jiya Lahadi a nan birnin Bonn.
Jamusawa dai na cigaba da nuna shakku dangane da nasarar irin wannan gwamnati ta hadin gambiza, musamman idan ya hada da manyan jam'iyyu na siyasa, kamar yadda Anita Braun ta nunar...
" Ba na murna da irin wannan gwamnatin hadaka. Dangane ta tattaunawa, ban san wane mataki ake ba, amma a gaba daya lamarin ba shi da dadi, domin wannan ba shi ne abun da muka kada kuri'a a kai ba".
Wasu na masu ra'ayin cewar a baya Jamus ta kasance cikin irin wannan gwamnati ta hadin gwiwar manyan Jam'iyya amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba a cewar wata Bajamushiya Heidi Meus...
" Tabbas, saboda mun ga irin wannan gwamnatin hadin gambiza ta manyan jam'iyyu a baya, amma ba ta tabuka komai ba. Ina ganin dai ya kamata a gudanar da sabon zabe kawai".
Amma a ra'ayin Marco Nizzare, wannan ce za ta kasance mafita ga kasa kamar Jamus, maimakon a tarin tsintsiya da ba za ta iya shara mai kyau ba...
" Ya ce gamayyar manyan jam'iyyu ta fi tarin kananan jam'iyyu. A nawa ra'ayin gwamnatin manyan jam'iyyu guda biyu ita ce za ta fi dacewa".
Wasu na tsoron cewar rashin cimma nasara kan muhimman batutuwa a bangaren SPD a tattaunawar da za su shiga , zai iya kara zubar da martabar jam'uyyar a idon duniya.
Ita kuwa Angela Merkel da ke hararar kujerar shugabancin gwamnati a karo na hudu, maraba ta yi da nasarar fara shiga mahawarar kafa gwamnatin hadakar..
" Idan aka zo batun kafa gwamnatin hadaka, batu ne da ke da muhimmancin garemu na samar wa Jamus ingantacciyar gwamnati, wadda za ta iya magance matsalolin da suka taso. A bangaren, karfin tattalin arziki, na daga cikin muhimman batutuwan da za mu mayar da hankali a kai, musamman a wannan lokaci da muke ciki domin tabbatar da adalci da tsaro".
Duk da wadannan mabanbantan ra'ayoyi dai kallo ya koma kan wadannan 'yan siyasa na ganin yadda za su gano bakin zaren cimma matsaya, wanda hakan ne zai share hanyar kafa gwamnati tun bayan zaben kasa a watan Satumban shekara ta 2017 a nan Jamus.