1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Mahawara kan 'yan gudun Hijira

Naomi Conrad/Ahmed SalisuJuly 26, 2016

Hare-haren da aka kai a Jamus sun janyo sake duba hanyoyin zaman 'yan gudun hijira a kasar tsakanin 'yan siyasa da sauran mutane.

https://p.dw.com/p/1JW6G
Nach Schießerei in München Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da tattara bayanai game da hare-hare na baya-bayan nan da aka kai wasu birane a nan tarayyar Jamus, a share guda wasu na duba yadda yanayi karbar baki musamman a Jamus zai kasance duba da yadda shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi fice wajen bude kofofin kasar ga baki 'yan gudun hijira.

Al'ummar gari da masu sharhi kan lamuran yau da kullum da ma 'yan siyasa na cigaba da tofa albarkacin bakunansu game da makomar karbar baki 'yan gudun hijira da Jamus ke cigaba da yi musamman ma a wannan lokaci da kasar ta fuskanci hare-hare da suka kai guda hudu a cikin makon da ya gabata wadanda galibin wanda suka kaisu ke da nasaba da yankin gabas ta tsakiya.

Mutane da dama dai na ta dari-dari kan yadda kasar da ma lamura za su kasance idan aka mika duba da yadda baki daga yankin gabas ta tsakiya suka fi na sauran sassan duniya neman mafaka a kasar, to sai dai ministan da ke kula da harkoki na cikin gida Thomas de Maizière ya ce batun tayar da hankali bai taso ba domin kuwa hukumomi sun dauki matakai na ganin lamura ba su kazance ba.

München nach Amoklauf am Olympia Einkaufszentrum Thomas de Maiziere
Hoto: Getty Images/J. Simon

A daura da wadannan kalami da ministan na cikin gida na Jamus ke yi, a hannun guda mahawara ce ake cigaba da tafkawa kan yanayi hare-haren da alakar da suke da ita da kungiyoyin da suka yi fice wajen aikata ta'addanci ciki kuwa har da kungiyar nan ta IS da ke rajin girka daular Islama a Siriya da Iraki da wasu sassa na yankin gabas ta tsakiya.

Wani kaso na al'umma da suka shiga wannan tattaunawa dai na gani wasu daga cikin wanda suka nemi mafaka a Jamus da ma wasu kasashen Turai na zaman mambobi na kungiyoyin 'yan ta'adda batun da ya sanya masu wannan ra'ayi ke ganin ya kamata hukumomi a nan Jamus su sake lale game da karbar baki 'yan gudun hijira, sai dai Ulrike Demmer mataimakaiyar mai magana da yawun shugabar gwamnatin kasar na ganin irin wadannan mutane sun yi wa wannan matsala gurguwar fahimta.

Deutschland Afghanische Flüchtlinge trauern um die Opfer des Anschlags in Kabul in Köln
Hoto: Iraj Akbari

Sai dai duk da wannan kalamai na Ms. Demmer wasu 'yan siyasa musamman ma wanda ke da ra'ayi irin na kyamar baki na ganin hanya daya da za ta zamaewa Jamus da ma Turai mafita kan irin hare-haren da suke fuskanta shi ne dakatar da karbar baki.