1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Jamus ta ce babu laifi a saka makakan corona

November 30, 2021

A Jamus kotun tsarin mulki ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar gabanta na halaccin tsauraran matakan corona da mahukuntan kasar suka saka a farkon wannan shekarar a kokarin yaki da cutar a karo na uku. 

https://p.dw.com/p/43fH6
Deutschland | Coronavirus | PK Ministerpräsidentenkonferenz
Hoto: Michael Kappeler/AFP/Getty Images

Kotun wacce ta yi zamanta na karshe a kan wannan batu a birnin Karlsruhe ta ce matakan da aka saka a wancan lokacin, duk da tsaurinsu da ma shiga hakkin walwala da kundin tsarin mulkin ya baiwa ko wane dan kasa, dokokin sun yi daidai da kundun mulki kasar.

Wannan mataki na kotun dai na zuwa ne a daidai lokacin da mahukunta a Jamus ke neman hanyoyin magance annobar corona a karo na hudu, wanda a gaba a yau ne shugabar gwamnatin Jamus mai barin gado Angela Merkel za ta gana da sabon shugaban gwamnati da ke tafe Olaf Scholz da kuma gwamnonin kasar 16 domin tattaunawa a kan matakan bai daya da zasu dauka.

Tuni gwamnan jihar Bavaria Markus Soeder ke kira da a hanzarta daukan matakan dakile wannan cuta musamman ma da bullar wannan sabon nau'in da ke da saurin yaduwa.

Sai dai al'umma da dama a Jamus na masu adawa da wasu dokoki da za a saka, lamarin da a baya ya kai su gudanar da bore a kan hakan.