Merkel ta sake fuskantar karkarwar jiki
July 10, 2019Talla
Saidai da take bayani a gaban 'yan jarida tare da Firaministan kasar ta Finland, Merkel ta ce tana cikin koshin lafiya. Sai dai ta ce ana yi mata bincike kan wannan matsala tata.
A ranar 18 ga Yunin da ya gabata ne Merkel da ke shirin cika shekaru 65 a ranar Laraba mai zuwa, ta fara fuskantar a karon farko wannan larura ta karkarwar jiki a lokacin da ta karbi bakuncin Shugaban Kasar Ukrain Volodymyr Zelenskiy a birnin Berlin, kafin matsalar ta sake dawo mata a ranar 27 ga watan na Yuni lokacin wata ganawa da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier awoyi kalilan kafi tashi zuwa taron koli na G20 a kasar Japan.