Karancin jami'an soji ya addabi Jamus
April 2, 2023Talla
Rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr na fama da karancin jami'an da za ta tura fagen daga, a cewar kwamishiniya mai kula da harkokin soji a majalisar dokokin kasar Eva Högl.
Jami'ar ta ce ya kamata adadin sojojin Jamus ya kai 203,000 daga nan zuwa shekaru bakwai masu zuwa. A yanzu haka dai rundunar sojin ta Jamus na da jami'ai 183,000, da a cewar Högl, ba su wadata ba.
Hukumomi sun ce ficewar da kuratan soji ke yi daga rundunar ta Jamus da kuma matakai masu tsauri a wajen daukar sabbin kurata ne ke kara haifar wa Bundeswehr din karancin sojoji.