Jamus na iya bai wa Edward Snowden mafaka ?
November 4, 2013Rawuwar Edward Snowden tsohon jami'in leƙen asirin na Amirka wanda yanzu haka ya sami mafaka ta siyasa a Rasha,ta kasance a cikin kewa ta rashin 'yan uwa da dangi da kuma sauran wasu abubuwa na rayuwa.To sai dai kuma ana hasashen cewar watakila Jamus ta kan yiyuwa ta ba shi mafakar siyasar, batun da kuma 'yan siyasa na Jamus ɗin suke ta yin tsokaci akai.
Abu ne mai yiwuwa a cewar wata yar Siyasar ta jam'iyyar masu kare muhalli
Wannan tunani dai ya biyo bayan ziyarar da wani ɗan siyasar ɗan majalisa na jam'iyyar masu fafutukar kare muhalli Hans Christian Ströbele ya kai wa Snowden ɗin a birnin Moscow inda ya gana da shi kana kuma suka tattauna, wanda a kan haka ake ganin a kwai buƙatar Snowden ɗin ya iso a Jamus kamar yadda yayi fata, domin ya bayyana a gaban wani kwamiti na musamman don ba da ƙarin haske a kan zargin da ake yi wa hukumar NSA da tatsar bayanan sirri na wayar salula ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, kafin daga bisani shi ma ministan cikin gida na ƙasar ta Jamus Hans-Peter Friedrich,ya ce a shirye suke su saurari tsohon jami'in na Amirka indan har ya zo. Abin dai yana da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, domin idan har Snowden ɗin ya kuskura ya yi balaguron to kam zai iya rasa matsayin da yake da shi na ɗan gudun hijira a Rasha. Sai dai kuma wani ofishin bincike na majalisar dokokin ta Jamus ɗin wato Bundestag ya ce ana iya a gewaye yarjejeniyar da ke tsakanin Amirka da ƙasashen Kungiyar Tarayyar Turai, na tisa ƙeyar masu laifin zuwa ƙasashen. Abin da kuma mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Claudia Roth ta ce yana yiwuwa a aikata shi a kan Snowden :'' A gare mu sigina ce mai kyau Edward Snowden ya iso Jamus zai kasance shaida a gaban kwamitin binciken, wanda muke yin fafutuka a kansa.''
Martanin ɓangaren gwamnatin a kan wannan danbarwar
A wani binciken da ta gudanar wata jarida ta nan Jamus Der Spiegel, ta ce kusan kashi 50 cikin 100 na al'ummar ta Jamus na buƙatar Snowden ɗin ya iso a Jamus don a yi masa tambayoyi Bernd Riexinger na jam'iyyar Linke na daga cikin waɗanda ke da írin wannan ra'ayi.Ya ce :''Snowden ya taimaka ga samin haske ga abin da hukumar leƙen asirin Amirka ta ke yi na satar wayoyin jama'a da shugabannin ko China ko Rasha ko wacce ƙasa ma ya kamata ta ba shi mafakar siyasa.'A yanzu shugabar gwamatin Jamus Angela Merkel ba ta ce komai ba dangane da wannan batun na ba da mafakar siyasar, to amma wani darakta a fadarta Michael Grosse Brömer ya mayar da martani, inda ya ce : ''Babu wata bita da ƙuli ta siyasa da ake yi masa kuma wannan buƙata ba ta cikin dokar kwamitin na iya zuwa Rasha domin sauraron Snowden ɗin''
Mawallafi :Taube Friedel/Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe