Mahawara kan janye sojin Jamus daga Mali
November 18, 2022Gwamnatin Jamus tana muhawara game da janye sojojin kasar na rundunar Bundeswehr daga kasra ta Mali da ke yankin yammacin Afirka, inda sojojin ke karkashin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira MINUSMA.
Ornella Moderan mai bincike kan lamuran duniya a wata cibiya da ke kasar Netherlands ta shaida wa DW cewa:
"Tun lokacin da Faransa ta kawo karshen dakarun Barkhane da na kasashen Turai na Takouba sannan Mali ta fice daga cikin kungiyar kasashen G5 Sahel , abin da ake tunani shi ne mahukuntan birnin Bamako sun kirkiri yanayin da dakarun kasashen ketere za su fice daga kasar kamar abin da ake fgani shi ne idan duk dakarun da suke fice daga Mali ba a maye gurbinsu lamarin da zai saka matsin lamba da wadanda suke aiki a kasar su ma su fice"
Yanzu haka kasashen Birtaniya da Cote d'Ivoire sun bayyana za su janye, kana kasar Masar ta janye tun farkon wannan shekara yayin da kasar Sweden ta ce za ta kajnye daga Mali a watan Yunin shekara mai zuwa ta 2023. Ita dai rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Mali tana da sojoji fiye da 15,000, kuma yanzu haka wasu yankunan na kasar na hannun kungiyoyin tsageru da 'yan ta'adda.
Christine Lambrecht ke zama ministar tsaron Jamus ga abin da take cewa kan batun:
"Masu mulkin Mali dole su yi bayani suna son ci gaba da aiki da kasashen dunyia kan yaki da ta'addanci inda suke maraba da su. Yanzu haka ina da shakku kan haka."
Idai Jamus ta nuna cewa ya dace dakarun kasra kimanin 1,400 su ci gaba da zama a kasar ta Mali saboda kare yankin na zama kariya har da kasashen Turai.
Anna-Lena Baerbock minsitar harkokin wajen Jamus ta ce akwai hadari da ake fuskanta a ynakin daga kungiyoyin masu ikirarin jihadi na hargitsa lamura ga kuma Rasha da ke neman samun tacewa a kasashen ynakin:
"Idan gaba daya yankin ya fada hannun masu matsanancin ra'ayin Islama, idan yara mata aka hana musu zuwa makaranta ko kuma gaba dayan Mali ta koma 'yar koran Rasha, lamuran za su shafe a kasashen Turai.
Sojojin da ke mulkin Mali na dasawa da gwamnatin Rasha, inda sojojin haya na Rasha na kamfanin Wagner kimanin 1,000 suke da tasiri a kasar ta Mali, kuma mai kamfanin sojojin hayan ya kasance makusancin Shugaba Vladimir Putin na Rasha. Sadio Camara minsitan tsaron Mali ya ce dangantaka tsakanin kasarsa da Rasha kowane bangare zai samu nasara.