1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta bukaci a bawa Taliban hadin kai

Abdul-raheem Hassan
September 8, 2021

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya ce dole kasahen duniya su amince da kungiyar Taliban bayan kafa gwamnati da sunayen wasu mutanen da Amirka ta yadda da su.

https://p.dw.com/p/405fx
Deutschland US-Außenminister Blinken trifft afghanische Flüchtlinge in Ramstein
Hoto: Michael Probst/AP Photo/picture alliance

Sai dai da yake martani a tattaunawarsu da Blinken a garin Ramstein da ke kudancin Jamus, Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce gwamnatin Berlin ba ta da kwarin gwiwa kan sabuwar gwamnatin Taliban, amma duk da haka Jamaus ta ji dadin taimakon Amirka wajen fitar da mutane daga Afganistan.

"Ina matukar farin cikin mun sami nasarar taimakon gwamnatin Amirka kwashe jama'a daga Kabul, kuma za mu ci gaba da aikin kwashe mutane da suka rage a Afganistan. Sanna za mu warware kulli da tambayoyi kan yadda abubuwa za su ci gaba a Afghanistan da yadda za mu sami matsaya ɗaya kan duk waɗannan batutuwan." Inji Maas

Wannan dai na zuwa ne yayin da sabuwar gwamnatin na Taliban ke fuskantar jerin zanga-zanga daga kungiyoyi da mata a ciki da wajen Afganistan inda wasu ke kukan cewa Taliban suna danne musu hakkinsu.