SiyasaGabas ta Tsakiya
Jamus ta bukaci a waiwayi yarjejeniyar nukiliyar Iran
January 20, 2022Talla
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken sun yi ittifakin cewa har yanzu akwai yiwuwar ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar Iran.
''Tattaunawar nukiliyar Iran din na cikin babban mataki. Muna bukatar ayi gaggawar ci gaba da ita, idan ba haka ba muradun takaita zirga-zirgar makamai da ake son cimma zai yi wuya a same shi.'' inji Baerbock
A watan Yunin shekarar da ta gabata aka fara farfado da yarjejeniyar dakile shirin makamashin nukiliyar Iran din ta 2015. Sai dai an dakatar da ita bayan da kasar Iran ta zabi Ebrahim Ra'isi da ake siffantawa da mai ra'ayin rikau a matsayin shugaban kasa.