1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus na tuhumar masu yunkurin juyin mulki a kasar

December 12, 2023

Mai gabatar da kara na gwamnatin Jamus ya gurfanar da mutanen nan 27 da ake zargi dan hannu a yunkurin kifar da gwamnati a bara.

https://p.dw.com/p/4a5ar
Hoto: HEIKO BECKER/REUTERS

Babban mai gabatar da kara na gwamnatin Jamus ya gurfanar da mutanen nan 27 ''masu tsattsauran ra'ayi'' da ake zargi da yunkurin kutsawa majalisar dokokin kasar da kuma kifar da gwamnati a bara.

Mutum 26 daga cikinsu ana zarginsu da hada kai da kungiyar nan mai tsattsauran ra'ayi dake Frankfurt, karkashin jagorancin hamshakin 'dan kasuwar nan Prince Heinrich XIII Reuss da kuma wata mace da ake zargi da goyon bayan kungiyar.

Duba da girman laifin da ake tuhumarsu da aikawata, manyan alkalan kotunan Frankfurt da Munich da kuma Stuttgart ne zasu jagoranci shari'ar mutanen da aka fi sani da Reichsbuerger.

A watan disambar shekara ta 2022, ne aka dakile ayyukan tsagerun na yunkurin kifar da gwamnatin Jamus da aka yi ta cece-kuce kan batun a jaridu daban-daban na duniya.

Babban mai gabatar da karar Peter Frank, ya ce daga cikin laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa akwai gudanar da haramtaccen gangami na kifar da gwamnati da kuma mallakar makamai da kuma kafa rundunar tsaro ta kashin kansu a Jamus, tare da yunkurin tsayar da  Prince Heinrich XIII  a matsayin sabon jagoran kungiyar, wanda yanzu haka ke tsare.