Zargin alakar Rasha da jam'iyyu a Jamus
February 14, 2019Cibiyar leken asirin cikin gida a Jamus ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan alakar Rasha da wasu jam'iyyu na kasar ciki kuwa har da jam'iyyar AfD mai adawa da baki a kasar ta Jamus, kamar yadda gungun kamfanonin yada labarai na RND suka ba da rahoto a wannan Alhamis inda suka bayyana majiyar labarin nasu daga jami'an leken asirin.
Cibiyar leken asirin ta Jamus a matakin tarayya BfV ta cimma matsaya da rassanta a yankuna don sa idanu kan wannan zargi tun daga ranar Talata bayan da aka samu rahotanni Rasha na son kutse kan harkokin zabe a kasashen Turai a watan Mayu, da ma wasu zabukan na yankuna uku da za a yi a gabashin Jamus a wannan shekara a cewar kafofin yada labaran na RND.
Zargin Rasha da kutse kan harkokin zabe a kasashen na yamma dai na ci gaba da karuwa, yayin da har kawo yanzu bincike bai tsaya ba kan zargin kasar ta Rasha da kutse kan harkoki na zaben Amirka a shekarar 2016.