Kalubalantar harkokin tsaro a Turai
February 18, 2022Talla
A daidai lokacin da shugabannin kasashen yamma ke fara wani taron tsaro na shekara shekara a birnin Munich na kasar Jamus a yau, ana ci gaba da fargabar yiwuwar Rasha ta mamaye Ukraine.
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta ce akwai bukatar Rasha ta nuna da gaske take wajen kawo karshen wannan takaddamar da aka kwashe lokaci ana yi. Ta kara da cewar Rasha na kalubalantar ka'idojin zaman lafiya na kasashen Turai.
Rikicin Rasha da Ukraine dai shi ne babban batun da zai mamye zauren taron tsaro na Munich, sai dai Rasha ta janye kanta daga halarta taron abin da ministar harkokin wajen Jamus din ta ce bai kamata ba.