1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici kan hakar ma'adinan kwal

Zainab Mohammed Abubakar
January 11, 2023

Hatsaniya ya barke tsakanin jami'an 'yan sanda da masu fafutukar kare muhalli a kauyen Lützerath, a kan aikin hakar ma'adinai kwal don bunkasa makamashi a fadin Jamus.

https://p.dw.com/p/4M16w
Deutschland Klimaaktivistinnen blockieren die Räumung von Lützerath
Hoto: Ina Fassbender/AFP

Kauyen da ke yammacin Jamus ya zama sabon wuri a baya bayannan da aka dade ana arangama tsakanin masu zanga-zangar kare muhalli da ke neman a sake tunani game da manufofin sauyin yanayi na mahukuntan kasar.

'Yan sanda, wadanda suka kasance a kewayen kauyen tun kwanakin baya, sun yi amfani da amsa-kuwwa wajen sanar da cewa duk wanda ke zama a cikin yankin dole ne ya fuskanci yiwuwar tilasta masa barin wurin.

Katafaren kamfanin samar da makamashi na RWE na da niyyar amfani da kauyen Lützerath mai nisan kilomita 40 da yammacin birnin Cologne, don hakar ma'adinan kwal a wani mataki na inganta samar da makamashi.