1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Jam'iyyar CDU na ci gaba da samun koma baya a Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe AAI
February 24, 2020

Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta samu koma-baya a zaben da ya gudana a Hamburg da ke arewacin Jamus, yayin da AFD da ke kyamar baki ta yi nasarar samun kujeru a majalisar dokokin jihar.

https://p.dw.com/p/3YLd4
Magajin garin Hamburg Peter Tschentscher kuma dan takarar da ya yi nasara a zaben
Magajin garin Hamburg Peter Tschentscher kuma dan takarar da ya yi nasara a zaben Hoto: Reuters/C. Mang

Wannan zaben da SPD ta samu nasara ya kasance na farko da aka gudanar a Jamus tun bayan rikicin siyasa da kasar ta fada a ciki bayan zaben jihar Thüringen. Jam'iyyar CDU mai ra'ayin mazan jiya ta Angela Merkel ta zo a matsayi na uku a zaben da ya gudana a Hamburg a ranar Lahadi, inda ta samu kashi 11% kacal na kuri'un da aka kada. Wannan sakamakon ya kasance koma baya ga jam'iyyar idan aka kwatanta da kashi 15.9% da ta samu a shekara ta 2015, sannan ya zama kaye mafi muni da ta samu a shekarun 69 na baya-baynan nan. Ita dai jam'iyyar da ke mulkin Jamus ta samu kanta cikin yanayi na tsaka mai wuya, tun bayan da masu ra'ayin rikau suka hada gwiwa da masu kyamar baki na AFD masu kyamar baki wajen zaben dan takara mai sassaucin ra'ayi a matsayin jogaroan jihar Thüringen da ke gabashin Jamus, lamarin da ya shafa wa CDU kashin kaji. Ga abin da Sakatare Janar na CDU Paul Ziemiak ke cewa kan zaben na Hamburg.

Kusoshinn jam'iyyar CDU tare da Angela Merkel kafin a ka'da kuri'a
Kusoshinn jam'iyyar CDU tare da Angela Merkel kafin a ka'da kuri'aHoto: Imago Images/E. Contini

"Zan yi magana kai tsaye ba tare da rufa-rufa ba: rana ce mara kyau ga jam'iyyar CDU. Wannan shi ne zabe mafi muni ga CDU a Hamburg, kuma babu wani abin boyewa."

Jam'iyyar SPD da ke kawance da ta Merkel a gwamnatin tarayyar ce ta fi samun kuri'u a zaben na Hamburg inda ta samu kashi 37,5% na kuri'un da aka kada. Wannan yana nufin cewa jam'iyyar da ke da matsakaicin ra'ayin rikau za ta yi hadin gwiwa wajen ci gaba da mulkin jihar da ke arewacin Jamus. Wannan dai shi ne zaben farko da jam'iyyar SPD ta lashe a baya-bayan nan, lamarin da ya faranta ran Saskia Esken, shugabar jam'iyyar SPD:

"Ta ce, tabbas wannan babbar nasara ce, saboda SPD a Hamburg za ta iya kafa gwamnati a kan kyakkyawar turbar dimukuradiyya, a bayyane take cewa sakamakon Thüringia bai zama ruwan dare a Jamus ba, kamar yadda Hamburg ta nuna a fili. Jama'ar Hamburg sun fara fahimtar raina bil'Adama da ke boye bayan manufofin AFD. "

Magajin garin Hamburg Peter Tschentscher kuma dan takarar da ya yi nasara a zaben
Magajin garin Hamburg Peter Tschentscher kuma dan takarar da ya yi nasara a zaben Hoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz


Ita dai AfD ta sami kashi 5.3% na kuri'un da aka kada a zaben Hamburg, lamarin da ya ba ta damar samun kujeru a majalisar jiha kamar yadda dokokin Jamus suka tanada. Sai dai jam'iyar da ke kyamar baki ta samu koma-baya idan aka kwantata da zaben da ya gudana a shekarar 2015, inda ta samu kashi 6.1% . Wannan nasarar dai ta kasance wa AFD bazata saboda ana zarginta da tunzura magoya bayanta da cin zarafin baki musamman ma Musulmi, lamarin da ya haddasa hare-haren wariyar launin fata a garin Hanau, inda mutane tara suka rasa rayukansu.

Sai dai jam'iyyar The Green da ke da rajin kare muhalli ta kasance daya daga cikin masu san barka a zaben Hamburg saboda ita ce ta zo a matsayi na biyu bayan da ta lashe kashi mai tsoka na kuri'un da aka kada. 'Yar takarata Katharina Fegebank ta nuna farin cikinta dangane da wannan sakamako.

Shugabar jam'iyyar Green Party Anna Gallina da 'yar takara su Katharina Begebank
Shugabar jam'iyyar Green Party Anna Gallina da 'yar takara su Katharina BegebankHoto: Getty Images/S. Gallup

 "A ko yaushe ina tsammanin jefa kuri'a, abu ne mai kyau. Kuma a yau zaben ya da'da'damin rai sosai. Ina aka waiwayi 'yan makonnin da suka gabata da kuma yadda yakin neman zabe ya gudana, ina farin ciki da sakamakon da muka samu da wannan maraice da karfe 6 na yamma. Kuma ina fata na gari."

Duk da fatan lamiri da suma suka yi wa kansu, masu sassaucin ra'ayi na FDP ba su da tabbacin samun kujeru a majalisar Hamburg, matukar ba ta samu kashi 5% na kuri'un da aka kada kamar yadda doka ta tanadar ba. Wannan jam’iyya ta kasance daya daga cikin wadanda suka haddasa rikicin siyasar jihar Thüringia, wanda ya sa gwamnatin tsakiya tangal-tangal. Idan za a iya tunawa dai, dan takarar jam'iyyar FDP ya karbi kujerar shugabancin yankin don goyon bayan 'ya'yan jam'iyyar CDU ta Merkel da kuma AFD da ke kyamar baki, ko da yake dai ya yi murabus daga bisani sakamkon matsin lamba.