1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: Shekaru biyar na "za mu iya"

September 1, 2020

Shekaru biyar ke nan da Jamus ta bude kan iyakarta ga dubun-dubatar 'yan gudun hijira, ko Jamus din ta cimma kalmar nan ta shugabar gwamnati wato "za mu iya"?

https://p.dw.com/p/3hrQm
Deutschland Berlin Flüchtlinge Warteschlange LAGESO
Kalmar "za mu iya," ta shugabar gwamnatin Jamus ta janyo kwararar 'yan gudun hijiraHoto: Reuters/F. Bensch

Za dai a iya cewa, tsawon shekarun da Angela Merkel ta kwashe a matsayin shugabar gwamnatin Jamus, ba ta taba furta wata kalma da ta yi tasiri irin na kalmarta dangane a batun 'yan guduun hijira ta "Za mu iya" ba. Wannan kalma tata ta bayar da kwarin gwiwa, inda cikin makonni kalilan da furta kalmar, dubban 'yan gudun hijira suka shigo Jamus, mafi yawansu ta kasasshen yankin Balkan, da yawansu wadanda suka makale ne a kasar Hangari. 

Mafiya yawa daga cikin 'yan gudun hijirar dai sun fito ne daga kasar Siriya, yayin da sauran suka fito daga kasashen arewacin Afirka da Iraki da kuma Afghanistan.

Karin bayani: EU- Samun mafita kan batun 'yan gudun hijira 

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bude kofa ga dukkan 'yan gudun hijirar, koda kuwa alhakin kula da su na kan wasu kasashe ne bisa ka'idojin karbar 'yan gudun hijira na kungiyar Tarayyar Turai EU, inda ake yin nazarin bukatarsu ta neman mafaka daga bisani tana mai cewa: "Jamus kasa ce mai karfi. Mun cimma nasarori da dama dangane da matakan da muka dauka wajen tunkarar wannan matsalar. Za mu iya, za mu iya. Kuma idan wani abu ya sha mana gaba, za mu kawar da shi."

Bundeskanzlerin Angela Merkel vor der Bundespressekonferenz Berlin 31 08 2015
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Imago/photothek/T. Imo

A shekara ta 2015 kadai,'yan gudun hijira sama da miliyan daya ne aka yi musu rijista a Jamus. Kalmar "za mu iya" ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bai wa mutane da yawa kwarin gwiwa.  An yi ta tataunawa ddangane da wannan kalmar a kafafaaen yada labarai na kasashen ketare kamar "New York Times" da Al-Jazeera.

Sai dai a wata hira da kafar yada labarai ta ARD ta Jamus ta yi da shi cikin wanna wata na Agusta, ministan cikin gidan Jamus din a wancan lokaci, Thomas de Maizière ya amince cewa akwai "lokutan da yanayin ya fi karfinsu," koda yake shi ma ya amince da cewa sun cimma nasara a tsawon shekaru biyar da matakin da Merkel din ta dauka kan 'yan gudun hijirar: "Mun cimma nasarori masu yawa. Mun rage dawainiyar samun mafaka, kuma a yanzu ba mu da wadanda ba su da gidajen kwana. Haka ma fannin kula a lafiya na aiki yadda ya kamata da taimakon kungiyoyin sa kai. A lokaci guda kuma akwai kalubale.

Karin bayani: Jamus ta ce za ta iya da 'yan gudun hijira

Akwai da yawa da ke karya doka kuma ba mu mayar da su zuwa kasashensu na asali ba, wasunsu sun ki shiga ajin Jamusanci domin daukar darasin sajewa. Tabbas akwai wadanda ke aikata manyan laifuka cikin masu neman mafaka, a dangane da haka aakwai sauran aiki a gaba."

Deutschland Vorstellung Verfassungsschutzbericht 2020
Ministan cikin gida na Jamus Horst Seehofer Hoto: Reuters/H. Hanschke

A nasa bangaren minsitan cikin gidan Jamus din na yanzu Horst Seehofer na jam'iyyar CSU da ke zaman abokiyar taakwaitakar jam'iyyar Merkel ta CDU, ya bayyana bude kofa ga 'yan gudun hijirar a 2015 da wani mataki na "rashin adalci." Jam'iyyun siyasar Jamus din dai na da ra'ayoyi mabambanta kan matakin na Merkel na shekara 2015.

Sharhi: Rikici kan 'yan gudun hijra a Jamus

'Yan siyasa daga jam'iyyun SPD da The greens da The Left da kuma FDP ba sa sukan Merkel kan wannan mataki, sai dai su na sukan sauran kasashen kungiyar EU da suka nuna halin ko in kula. A hannu guda 'ya'yan jam'iyyar AfD da ke da ra'ayin kyamar baki, sun nunar da cewa kamata ya yi Merkel din ta yi watsi da bukatar 'yan gudun hijirar. A cewarsu, hakan zai sanya a samu karancin bakin haure da ke yin kasada da rayuwarsu domin shigowa Turan.

Yayin da wasu ke taka tsan-tsan suna ganin Jamus ta kirawa kanta ruwa, wasu kuma na tambayar wacce riba za ta ci da wannan matakin, ganin cewa za ta fuskanci tarin mutane da suke da mabambantan al'adu. Za dai a iya cewa babu wata kalma da Merkel ta yi amfani da ita da ta raba kan 'yan kasar dangane da batun 'yan gudun hijira kamar wannan kalma ta "za mu iya." Kimanin kaso 60 na al'ummar kaasar dai na ganin kasar za ta iya kamar yadda Merkel ta fada, yayin da kaso 40 suke da wani ra'ayi na dabam. A siyasance jami'iyyar AfD ta masu ra'ayin kyamar baki, na kara samun tagomashi, abin da ake alakantawa da matakin shugabar gwamnatin kan 'yan gudun hijira.