1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Shin karshen mulkin Merkel ya zo ne?

Pohl Ines Kommentarbild App
Ines Pohl
September 26, 2018

Sauyin da aka samu na shugabancin kungiyar 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na nuni da yadda shugabar ke kokarin rasa karfin fada a ji a tsakanin 'yan jam'iyyarta.

https://p.dw.com/p/35Y9H
Bundeskanzlerin Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/M.Sohn

Kungiyoyi 'yan majalisu na jam'iyyun siyasa daban-daban kan cimma nasarar da suka sanya a gaba ne idan al'umma na da karancin sani akan irin baubuwan a suke aiwatarwa. A tsarin siyasar Jamus, irin wadanan kungiyoyi ne ke wucewa gaba wajen ganin sun sama wa shugabansu rinjaye a cikin kungiyar, sannan idan ya kasance sune ke rike da madafun iko to su kan taimaka wajen ganin shugaba ya yi aikinsa ba tare da fuskantar kalubale ba.

 

To sai dai duk da wannan kusan a iya cewar lamura sun cije a gwamnatin Jamus musamman idan aka dubi abin ta fuskar tsawon lokacin da aka dauka kafin a girka gwamnatin hadaka da kuma irin yadda wasu suka rika ajiye aiki da ma barazanar da ake ci gaba da fuskanta ta kaiwa ga rushe gwamnati da yin sabon zabe. Yanzu haka an kusa cika shekara guda bayan kafa gwamnati, akwai alamun kaiwa ga rushewar gwamnati mai ci wanda hakan zai haifar da fafutukar kafa sabuwar gwamnati.

Unionsfraktion im Bundestag -  Ralph Brinkhaus (CDU), stellvertretender Fraktionsvorsitzender der CDUCSU Fraktion
Ralph Brinkhau sabon shugaban rukunin 'yan majalisar dokoki na CDUHoto: picture-alliance/dpa/K.Nietfeld

Wannan dai na faruwa ne ba wai don kiki-kaka din da ake samu tsakanin jam'iyyun da suka yi kawance wajen kafa gwamanti ba ko kuma yadda jama'a suka dawo daga rakiyar jam'iyyun ba sakamakon rikicinsu na cikin gida da ke da nasaba da rikon madafun iko ba, Angela Merkel ta rasa irin gagarumin goyon bayan da ta ke da shi a rukunin ‘yan jam'iyyarta da ke majalisar dokoki ta Bundestag don kuwa sauke shugaban kungiyansu kana na hannun damanta wato Volker Kauder daga matsayinsa a wani abu ne da za a iya dangantawa da juyin mulki na cikin gida.

Hakan dai zai iya kaiwa ga yanayin da za a gudanar da sabon zabe ba tare da Merkel ba, wacce ake kallo a matsayin wadda ta kawo sauye-sauye a Jamus da ma Turai a iya tsawon shekaru 13 da ta yi kan madafun iko. Zaben da aka yi wa masanin tattalin arzikin Ralph Brinkhaus a mastayin shugaban 'yan kungiyar 'yan majalisa na jam'iyyar CDU daidai lokacin da Shugaba Donald Trump na Amirka ya caccaki Jamus a jawabinsa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya sanya da dama sake yi wa Jamus din wani kallo na daban.

Ines Pohl Kommentarbild App
Ines Pohl babbar Editar DWHoto: DW/P. Böll

Da dama daga cikin mambobin gwamnatin Jamus ba su kai ga fahimtar nauyin wannan yanayin da aka shiga ba. Al'ummar Jamus dai sun zabesu ne kan su yi aikin da zai ciyar da kasar gaba ba wai su dakatar da aiyyukan gwamnati na tsawon makonni ba kan takaddamar da ba za ta amfana musu komai ba sai kara karfi ga jam'iyyar AfD da ke kyamar baki.

Tun da fari, gwamnatin Jamus ba ta da wani kyakkyawan tsari a siyasance da ma fitattun mutane da kasar ke bukata wajen jagorantar kasar a lokutan da lamura suka dagule. Shugaba guda da ka iya wannan aiki mai cike da sarkakiya ita ce Merkel sai dai ita din ma ta rasa wannan matsayi domin ita ce da kanta ta haifar da rarrabuwar kawuwan da ake da su a gwamnatin hadakar da ta ke jagoranta da ma jam'iyyarta.

Yanzu dai ta faru ta kare domin kuwa mambobin jam'iyyar Merkel din ta CDU da abokiyar kawancenta ta CSU da ke jihar Bavaria sun yi illa babba a gareta, baya ga kawar da Kauder da suka yi daga matsayinsa na shugaban 'yan majalisar dokoki na CDU. Shin karshen mulkin Merkel ya zo kenan? Ko da wannan ba shi ne abin dubawa ba, abin da za a maida hankali a kai shi ne lokacin da mulkinta zai fadi.