1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban zaben Jamus na 2021

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 23, 2021

A karon farko bayan shekaru 16 a kan karagar mulki, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merekel ba za ta tsaya takara a zaben da za a gudanar a ranar 26 ga wannan wata na Satumba ba.

https://p.dw.com/p/40lHQ
Grafik aus Video zur Bundestagswahl
Hoto: DW

Zaben na ranar 26 ga wannan wata na Satumba dai, ba shi ne zai nuna kai tsaye wanda zai gaji shugabar gwam,natin Angela Merkel ba. Bayan an gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin ta Bundestag, jam'iyyar da t samu nasara ce za ta kafa gwamnati, ta yadda dan takararta zai kasance shugaba ko kuma shugabar gwamnati. Sai dai masharhanta na nuni da cewa, zai yi wahala a kafa gwamnati tsakanin jam'iyyun da suka jagoranci gwamnatin hadaka a lokacin Angela Merkel.

Bayan kwashe tsawon shekaru 16 a kan madafun ikon shugabar gwamnati a Jamus, Angela Merkel ta bayyana cewa ba za ta sake tsayawa takara ba. A lokacin mulkinta, Merkel ta cimma tarin nasarori musamman ta fuskacin tattalin ariziki. Sai dai batun 'yan gudun hijira da ta budewa kofofinta a a shekara ta 2015, ya kasance babban kalubalen da ta fuskanta. Ana dai ganin batun na 'yan gudun hijira na daga cikin dalilan da ya sanya Merkel cewa ba za ta sake tsayawa takara ba.  da ta