1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jinjnawa irin goyon bayan da al'umma suka bayar a Jamus

Zulaiha Abubakar
May 30, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana farin cikin game da nasarar kasar a yaki da annobar COVID-19 ya zuwa yanzu, tare da jaddada aniyar gwamnati ta ci-gaba da yaki da yaduwa ko sake billar cutar.

https://p.dw.com/p/3d2n9
Deutschland Berlin | Pressekonferenz Angela Merkel
Hoto: Getty Images/O. Messinger

Wannan jawabi guda ne cikin sakwannin mako-mako da shugabar gwamnatin ke yiwa al'umma ta bidiyo, sakon ya kunshi godiya ga da dama daga cikin al'ummar kasar wadanda ta bayyana a matsayin masu biyayya da mutunta umarnin shugabanni domin kowa ya tsira da lafiyarsa, a lokacin da al'ummar wasu kasashen ke korafi game da dokar zaman gida da hana zirga-zirga saboda annobar ta COVID-19, sai dai ta tsoratar game da masu yada jita-jitar cewar Jamus ta tsallake matakin yawaitar mace-mace kamar yadda wasu kasashen suka fuskanta. Bukatar gwamnatin kasar ta tsawaita bayar da tazara tsakanin al'umma har ranar 29 ga watan Yuni mai kamawa ta samu amincewar shugabannin jihohi 16 na kasar kodayake jagoran jihar Thüringen, Bodo Ramelow ya bukaci gwamnatin Jamus ta rage tsawon wa'adin bayar da tazarar tsakanin jama'a.

 

Sabon rahoton da cibiyar Robert Koch da ke nan Jamus ta fitar a wannan Asabar din ya bayyana cewar mutane  (181,196) ne suka kamu da cutar corona a nan Jamus daga ciki an samu asarar rayuka (8,489).