SPD ta yi kuri'ar na'am da ci gaba a kawancen mulki
December 6, 2019Duk da amincewar a share daya jam'iyyar ta bukaci buda wani fage na tattaunawa game da muhimman batutuwan da suka shafi tarin siyasar shugabar gwamnati Angela Merkel kan muhalli da karin albashi hakan da batutuwan zuba makudan kudade wajen inganta harkokin ma'aikatun gwamnati.
Ba tun yau ba dai sabbin shugabannin jam'iyyar ta SPD ke yin kakkausar suka ga tsarin siysar shugabar gwamnatin Angela Merkel game da batun na muhalli da na basusuka, inda suke fatan samun zarafi na tattaunawa ta zahiri kan batutuwan biyu da abukanin kawancensu na mulki wato CDU da CSU.
A karshen makon jiya ne dai aka zabi masu zazzafar suka ga ga kawancen Saskia Esken da Norbert Walter-Borjans a matsayin sababin shugabannin jam'iyyar da kuri'u mafi rinjaye bayan sun doke abokin hamayyarsu mai mukamin minista a cikin gwamnatin kawancen Olaf Scholz.