1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: SPD ta yi nasara a zaben Brandenburg

Abdullahi Tanko Bala
September 22, 2024

Sakamakon farko na zaben majalisar dokokin jihar Brandenburg a Jamus ya nuna Jam'iyyar Social Democrats ta shugaban gwamnatin Olaf Scholz ta sami ta sami nasara da tazara kankani akan Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki

https://p.dw.com/p/4kxEE
Jagoran Jam'iyyar SPD a Brandenburg
Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Sakamakon farko na zaben majalisar dokokin jihar Brandenburg a Jamus ya nuna Jam'iyyar Social Democrats ta shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ta sami ta sami nasara da tazara kankani akan Jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki.

Zaben ya gudana makonni uku bayan nasarar da Jam'iyyar AfD ta samu a jihohi biyu na gabashin Jamus.

Sakamakon ya nuna Jam'iyyar Social Democrats ta sami kashi 31 cikin dari na kuri'iun da aka kada yayin da AfD ta sami kashi 10 cikin dari.

Mutane miliyan biyu da dubu dari daya suka yi rajistar kada kuri'a a zaben sabbin 'yan majalisun dokokin na jihar Brandenburg da ke kewaye da Berlin babban birnin tarayyar Jamus.

.