Jamus ta amince da shirin samun mafaka
October 16, 2015Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da shirin shugabar gwamnati Angela Merkel kan tsaurara dokokin samun mafaka a kasar, da suka hada da mayar da 'yan kasashen yankin Balkan gida, saboda ba sa cikin kasashe da ke bukatar kariya. Kasashen sun hada da Albaniya, da Kosovo da kuma Montenegro. Sannan za a hanzarta kula da tarkardun wadanda suka fito daga kasashen da ake samun rikice-rikice kamar Siriya.
Tuni babbar majalisar dokoki, ta Bundesrat, wadda ta kunshi gwamnoni jihohi 16 na kasar, ta amince da ayar dokar bayan karamar majalisa ta Bundestag ta amince a wannan Alhamis da ta gabata. Wani hasashen gwamnati ya nuna yuwuwar fiye da masu neman mafaka 800,000 za su saka kafa a kasar ta Jamus, wadda ke daya daga cikin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki.