1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta amince da tura kayan yaki ga Ukraine

Suleiman Babayo LMJ
February 27, 2022

A karon farko cikin shekaru masu yawa Jamus ta amince da tura makamai inda ake yaki abin da ke zama sauyi manufofin kasar sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.

https://p.dw.com/p/47fGS
Bundeskanzler Olaf Scholz
Hoto: Tobias Schwarz/AFP/Getty Images

An samu gagarumin sauyi a manufofin Jamus kan yake-yake, inda gwamnati ta amince da tura kayan yaki ga sojojin Ukraine domin kare kansu da kasarsu daga kutsen da Rasha ta kaddamar. A baya Jamus ba ta makamai a wurare da ake yaki saboda neman hanyar diflomasiyya bisa warware rikice-rikice.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce cikin hanzari kasar za ta tura makamai da suka hada da na kariya gami da kakkabo jiragen saman yaki.

Tuni Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine wanda yake cikin mawuyacin hali ya yi maraba da matakin na Jamus.

Hakazalika, kasashen Amirka, Kanada, Italiya, Birtaniya da kungiyar kasashen Tarayyar Turai gami da Jamus sun amince da saka takunkumi kan bangaren tsarin kudin kasar Rasha sakamakon wannan kutse da ta kaddamar a kan Ukraine.

Amincewa da cire wasu bankunan Rasha daga tsarin kudi na bankunan duniya na daga cikin gagarumin sauyi daga bangaren Jamus wadda tun farko ta nuna rashin gamsuwa amma daga bisani ta amince saboda yadda shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gaban kansa tare da watsi da duk wasu hanyoyin diflomasiyya wajen kaddamar da kutse a kan Ukraine.