EU ya dace ta dauki matakai kan 'yan gundun hijira
November 9, 2021Ministan harkokin cikin gidan Jamus Horst Seehofer ya ce kasashen Jamus da Poland kadai ba sa iya kare kansu daga barazanar kwararar 'yan gudun hijira ba, saboda hakan dole kungiyar EU ta dauki mataki.
Jamus na goyon bayan duk wasu matakan da Poland din ke dauka a cewar ministan a yayin da yake zantawa da jaridar Bild, ciki har da kafa shingayen da ke hana masu yunkuri tsallakawa. Wannan dai na zuwa ne a yayin da kasar Poland din ta ce ta dakile kwararar bakin haure da 'yan hijirar Belarus da dama daga iyakokinta a yunkurinsu na shiga Turai ba kan ka'ida ba.
Kungiyar Tarayyar Turai ta zargi shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko da taimakawa bakin haure da 'yan gudun hijira, musamman daga yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin ramuwar gayya kan takunkumin da Brussels ta kakaba mata.
Ko a wannan Litinin ma dai kungiyar tsaro ta NATO ta soki gwamnatin birnin Minsk saboda amfani da bakin hauren a matsayin ‘yan amshin shata.