1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta cafke masu yi wa China leken asiri

April 22, 2024

Masu shigar da kara a Jamus yi nasarar cafke Jamusawa uku da ake zargi da yi wa hukumar leken asirin China aiki, ta hanyar satar bayanan sirri da kuma muhimman takardu da fasaha.

https://p.dw.com/p/4f3le
Wata ma'aikaci da ke satar bayanai ta na'urar kwamfuta
Wata ma'aikaci da ke satar bayanai ta na'urar kwamfutaHoto: Przemek Klos/Zoonar/picture alliance

Masu shigar da karar sun yi amannar cewa mutanen uku suna da hannu wajen ayyukan bincike da za su taimaka wa China ta fadada karfin tsaron ruwanta.

Karin bayani: Jamus ta kama masu yi wa Rasha leken asiri

'Yan sanda sun kama mutanen ne a  biranen Dusseldorf da Bad Homburg dake yammacin Jamus. Ana kuma binciken gidaje da wuraren ayyukan mutanen da ake zargi.

Karin bayani: Jamus ta zargi Rasha ta satar bayanan rundunar sojojinta

An bayyana cewa hukumomin China ne suka dauki nauyin ayyukan binciken da ake zargin mutanen da gudanarwa, to amma ya zuwa yanzu dai China bata ce uffan ba kan wannan batu.

Ko da a makon da ya gaba ma dai 'yan sandan Jamus sun kama wasu mutum biyu da aka zarga da yi wa Rasha leken asiri.