1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba a sa rai masu gadin Erdogan za su halarci taron G20

Mohammad Nasiru Awal AS
June 26, 2017

Ana zargin wasu masu tsaron lafiyar Shugaba Erdogan da cin zarafin masu zanga-zanga lokacin ziyarar da ya kai Washington.

https://p.dw.com/p/2fRAB
Türkei Recep Tayyip Erdogan in Istanbul
Hoto: Reuters/M. Sezer

A wannan Litinin Jamus ta ce ba ta sa rai jami'an tsaro da na 'yan sandar Turkiyya da ake zargi da cin zarafin masu zanga-zanga a birnin Washington, za su rako shugaban Turkiyya Tayyip Recep Erdogan zuwa kolin kungiyar kasashen G20 da zai gudana mako mai zuwa a birnin Hamburg na arewacin Jamus.

Bayanin zargin da ake wa wasu daga cikin masu tsaron lafiyar Shugaba Erdogan ya fito ne bayan wani hargitsi da ya auku a ranar 16 ga watan Mayu lokacin ziyarar da Erdogan ya kai babban birnin na Amirka, inda aka ji wa masu zanga-zanga tara rauni a wajen gidan jakadan Turkiyya.

Martin Schäffer shi ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus da ya ce dokokin Jamus za su yi aiki a kan jami'an tsaron matukar sun shigo kasar.

Ya ce: "Ba zan so in yi bayani dangane da abinda ya faru a Washington lokacin ziyarar shugaban Turkiyya ba. Amma ina tabbatar da cewa a dalilin wannan lamari wasu daga cikin tawagar shugaban Turkiyya musamman masu tsaron lafiyarsa, akwai sammacin da duniya ta bayar na kamasu."

Da ma dai a watannin baya-bayan nan huldar dangantaka tsakanin Jamus da Turkiyya ta yi tsami.