1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ce sam ba za a sake fasalin tsarin kudin Turai ba

April 27, 2012

Gwamnatin Jamus ta yi fatali da bukatar yin gyara ga tsarin tafiyar da ayyukan kudi na kasashen Kungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/14mI1
Bundeskanzlerin Angela Merkel begrüßt am Mittwoch (21.03.2012) auf der Integrationsministerkonferenz im Hotel Linsler Hof in Überherrn (Saarland) die zuständigen Minister und Senatoren der einzelnen Bundesländer. Bei der zweitägigen Konferenz im saarländischen Überherrn beraten die zuständigen Minister aus Bund und Ländern über Probleme bei der Integration von Migranten in Deutschland. Foto: Oliver Dietze dpa/lrs +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi watsi da sukan da ake yi game da shirin daidata tsarin kudi na kasashen Kungiyar Tarayyar Turai. A cikin hira da kamfanin yada labarun WAZ ya yi da ita Merkel ta ce tuni kasashe mambobin kungiyar guda 25 suka rattaba hannun kan yarjejeniyar da za ta tafiyar da harkar kudaden kasashen kungiyar, kuma ba za a sake tattauna wannan batu ba.

Merkel ta kuma yi amfani da wanan dama ta mai da martani ga kalaman Francois Hollande, dan takarar zaben shugaban kasar Faransa. Shi dai Hollande mai ra'ayin gurguzu ya yi alkawarin yin fatali da shirin tsuke bakin aljihu ko ta halin kaka yana mai yin suka ga matakan da shugaba Nikolas Sarkozy da Angela Merkel ke dauka wajen tinkarar matsalar bashi da ke addabar kasashen Turai. To amma Merkel ta ce za ta yi hadin-gwiwa da duk wanda ya lashe zaben shugaban kasar ta Faransa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu