Jamus ta dage kan aikin turo mata gas daga Rasha
December 3, 2018Kasar Jamus ta ce za ta ci gaba da aikin nan na shimfida bututun gas daga Rasha zuwa Jamus din da ake wa lakabi da North-Stream na biyu, duk kuwa da zafin takaddama tsakanin Rashar da Ukraine a yanzu.
Ana dai cece kuce kan wannan aikin shimfida bututun gas din da zai ratsa ta kasar Ukraine.
Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya fada a birnin Berlin cewa Rasha ta ba da tabbacin cewa bututun turo gas din zai ratsa ta Ukraine kamar yadda aka tsara tun farko, wato ke nan gwamnati a birnin Kiev ba za ta rasa gaba daya kudaden shiga da ta za ta samu dangane da wannan aiki ba.
Aikin na North Stream na biyu da zai yi jigilar gas kai tsaye daga Rasha zuwa Jamus yana shan suka da kakkausan lafazi daga kasar Amirka da ma wasu kasashen Turai bisa fargabar cewa ba zai ratsa ta Ukraine ba.