Jamus za ta bunkasa tattalin arzikinta
June 2, 2020Talla
Biyo bayan ta'annatin da annobar Corona ta yi wa tattalin arzikin kasashe a fadin duniya, Jamus ta lashi takobin farfado da tattalin arzikinta.
Babban batun da ake gani ka iya mamaye tattaunawar da ministocin kasar suka shirya shi ne batun kamfanonin kera motoci da ke kan gaba wajen bai wa al'umma aiki a kasar, wanda mai magana da yawun jam'iyyar SPD ya ce zai yi matukar wuya a samu matsaya a wannan ranar.
Takaddamar da ta barke tsakanin bangaren jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta Angela Markel da ke da ra'ayin rage haraji da kuma sassautawa 'yan kasuwa da kuma jam'iyyar 'yan gaba dai-gaba dai ta SPD da ke ganin a damkawa kowa tallafinsa a hannunsa shi ne mafi a'ala.