1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta fara kosawa da batun bashin Girka

Gazali Abdou TasawaJune 17, 2015

Fadar gwamnatin Jamus ta soma magana game da ficewar kasar ta Girika daga gamaiyar kasashen Turai masu amfani da takardun kudin Euro.

https://p.dw.com/p/1Fijr
Symbolbild Griechenland Schuldenkrise
Hoto: Reuters/Y. Behrakis

Daukacin Jamusawa sun gaji da batun bashin kasar Girka da ya ki ya ki cinyewa. Yanzu haka ma a fadar gwamnatin Jamus da ke birnin Berlin ana magana game da ficewar kasar ta Girika daga gamaiyar kasashen Turai masu amfani da takardun kudin Euro. Sai dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na mai ra'ayin cewa za a gano bakin zare warware matsalar.

Deutschland Bundeskanzlerin Angela Merkel mit Handy
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Schmidt

'Yan siyasa daga gwamnatin kawance ta Jamus wato CDU da CSU da kuma SPD na da ra'ayi wasu ma na fatan kawo karshen tattaunawa da ake tsakanin Girka da masu ba ta rance na kasashen EU da babban bankin Turai da kuma Asusun ba da lamuni na duniya IMF. Wani binciken jin ra'ayin jama'a da wata tashar telebijin din Jamus ta gudanar ya nuna cewa kashi 41 cikin 100 na Jamusawa ne ke kaunar ci gaba da ganin Girka a cikin kasashe masu cin kudin Euro. Duk da cewa akasarin Jamusawa sun fara nuna gajin hankuri ga batun bashin Girka, shugabar gwamnati Angela Merkel ta ce za ta yi iya kokarin ganin kasar ta Girka ta ci gaba da zama cikin dangi.

Griechenland Treffen Faymann Tsipras
Hoto: Reuters/P. Hanna

Ta ce: "Zan ba da tawa gudunmawa don ganin hukumomin nan guda uku sun cimma maslaha da kasar Girka don zama ginshikin tattaunawa da ministocin kudi na kasashen Eurogroup. Na sha fadan cewa zan yi duk abin da zan iya da bai fi karfi na ba, don mu rike Girka a cikin kasashen Eurozone masu amfani da kudin bai daya na Euro. Wannan aikin na dora ma kai na a cikin kwanakin nan."

To sai dai duk da haka dai a fagen siyasar a Berlin ana kara sukar lamirin gwamnatin Girka, inda ma aka jiyo mukaddashin shugabar gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel na zargin mahukuntan birnin Athens da tursasawa tare kuma wasa da hankalin mutane yana mai kwatanta alkawuran zabe da gwamnatin Girkar ta yi da wani abu mai kama da manufofin gwamnatin kwaminisanci, da Jamusawa ba za su dauki nauyin samar musu da kudaden cika wadannan alkawura ba.

Sai dai jam'iyyar 'yan ra'ayin sauyi wato Linke da ke zama jam'iyya daya tilo a birnin Berlin da har yanzu ke bayan gwamnatin Girka ta zargi Sigma Gabriel da amfani da matsalar Girkan don neman suna. Masu lura da al'amuran yau da kullum na zaton cewa mukaddashin na shugabar gwamnatin Jamus kuma dan jam'iyyar SPD ya yi amfani da wadannan kalamai masu tsauri don dakushe farin jinin Angela Merkel.

Sai dai hatta daga bangaren jam'iyar adawa ta The Greens an samu canji matsayi inda suke sukan take-taken gwamnatin Girka na tafiyar haiwaniya a kan batun bashin. Cem Özdemir daya ne daga cikin shugabannin jam'iyyar ta The Greens.

 

Ya ce: "Bai kamata mu dauke wa gwamnatin Girka musamman ministan kudin kasar nauyin da ke kansa ba. Dole ne suna cewa da gaske suke wajen aiwatar da sauye-sauye kuma dole ne a ga haka a zahiri. A hannu daya kuma na goyi bayan matsayin shugabar gwamnati cewa idan Girka ta fice daga kasashen masu amfani da kudi bai daya na Euro, matsayin kungiyar tarayyar Turai musamman na kasashen Eurozone zai fada cikin hadari."

Yanzu haka dai gwamnatin Girka ta dora fata kan samun wata maslaha a taron kolin EU da zai gudana ranakun Alhamis da Jumma'a na mako mai zuwa wato kwanaki kalilan gabanin wa'adin shirin tallafin da ake ba ta ya kare.