Jamus ta gargadi Rasha kan batun mamaya a Ukraine
January 17, 2022Shugaban gwamnatin na Jamus, Olaf Scholz, ya ce abin damuwa ne matuka kokarin mamaya da Rasha ke yi a gabashin Ukraine ganin dakarun nan da ta jibge a iyakar kasashen.
Yayin wani taron manema labaru a birnin Madrid na kasar Spain a wata ziyarar da ya kai kasar, Olaf Scholz ya ce matakin na Rasha ka iya janyo babbar matsalar tattalin arziki da na siyasa a tsakaninsu.
Ita ma ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, ta yi wannan gardi a ziyarar da ta kai Ukraine a wannan Litinin.
Su ma dai sauran wasu manyan kasashe musamman Amirka da na nahiyar Turai, na kokari ganin an kashe wutar rikicin da Rashar ta kunna.
Da ranar yau ne dai shugaban gwamnatin gwamnatin na Jamus ya kai ziyara a Spain, domin tattauna batutuwa da dama a tsakaninsa da Firaminista Pedro Sanchez.