Jamus ta goyi bayan hari kan Siriya
April 14, 2018Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar a ranar Asabar din nan cewa gwamnatinta ta goyon bayan harin da abokan kawancensu suka kai cibiyoyin gwamnatin Bashar Al-Assad na Siriya, inda ta ce hari ne da ta kamata kuma wanda ya dace bayan hari da makami mai guba da ake zargin gwamnatin ta Siriya ta kai a makon da ya gabata a birnin Douma wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce matakin na soja abu ne da ta kamata, kuma da ya dace domin a samu karewa da kuma hana duk wani amfani da makami mai guba, sannan da jan kunnen shugaban na Siriya kan aikata irin wannan aika-aikar a nan gaba.
Shugabar ta Jamus ta ce bisa dukkan alamu dai Gwamnatin Bashar Al-Assad ce ta kai harin na ranar bakwai ga watan Afrilu a birnin na Douma wanda a lokacin yake a hannun 'yan tawaye. Sai dai kuma a ranar Alhamis Shugabar gwamnatin ta Jamus ta sanar da cewa Jamus ba za ta shiga sahu wajen daukar matakin sojan ba.