1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta kare kanta a kotun duniya kan yakin Gaza

Abdullahi Tanko Bala
April 9, 2024

Nicaragua ta kai karar Jamus a kotun duniya kan zargin taimaka wa Israila aikata kisan kare dangi a Gaza, zargin da Jamsu din ta musanta.

https://p.dw.com/p/4eaS2
Zaman Shari'ar Nicaragua da Jamus a kotun duniya da ke Hague
Zaman Shari'ar Nicaragua da Jamus a kotun duniya da ke HagueHoto: Dursun Aydemir/Anadolu/picture alliance

Jamus ta zargi Nicaragua da karkata ga bangare guda kan batun yakin Israila da Hamas.

Jamus din na kare kanta ne a kotun duniya da ke Hague game da karar da Nicaragua ta shigar cewa taimakon da Jamus ke bai wa Israila ya taimaka mata aikata kisan kare dangi da karya dokokin kasa da kasa a Gaza.

Jagorar tawagar lauyoyin Jamus Tania von Uslar-Gleichen ta ce karar da Nicaragua ta shigar ta kauce wa gaskiyar lamura da dokokin shari'a.

Ta ce an shigar da karar cikin gaggawa kan hujjoji marasa inganci a saboda haka ya kamata a yi watsi da karar saboda rashin makama.

Shi ma da yake nasa tsokaci daya daga cikin lauyoyin na Jamus Christian Tams ya yi bayani da cewa O-Ton....

"Yace ba daidai bane sam a ce Jamus ta juyawa Falasdinawa baya. Jamus ta na aiki da abokan hulda da dama ta kafofi masu yawa kuma ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen saukaka wahalhalun da ake fuskanta."