Karfafa dangantakar Jamus da Faransa
January 22, 2019Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, sun saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar kara dankon zumuncin ne albarkacin cika shekaru 56 da saka hannu a yarjejeniyar da ta gabata tsakanin kasashen biyu da aka yi a birnin Paris na Faransa. Sabuwar yarjejeniyar za ta tabbatar da kammala duk abubuwan da aka amince da su lokacin yarjejeniyar shekara ta 1963, inda za ta kara karfafa danganta kan siyasa da tattalin arziki da hadin kai da walwalar al'umma gami da tabbatar da tsaro tsakanin iyakar kasashen biyu.
Yarjejeniya bayan zaman doya da manja
Yarjejeniyar ta wancan lokaci dai, an kulla ta ne tsakanin kasashen da a baya suka yi zaman doya da manja. Shin wadanne sababbin abubuwa ake ganin wannan yarjejeniyar za ta kara daga yanayin da ake ciki? Armin Laschet shi ne Firimiyan jihar North Rhine-Westphalia inda garin Aachen da aka saka hannu kan yarjejeniyar ke ciki, ya yi karin haske:
"Yarjejeniyar Aachen an danganta ta da wadda aka kulla a shekarar 1963. A wancan lokacin mataki na farko ne na sasantawa da kusantar juna tsakanin kasashen biyu. Yanzu kuma an duba abubuwa na zamanin da ake ciki kamar fasahar na'ura da dagnataka kan manufofin tsaro da kimiyya gami da bincike. Yarjejeniya ce ta karni na 21, Jamus da Faransa suna kusa da juna sosai."
Sabunta yarjejeniya bayan shekaru 56
Akwai dai matsala da ake samu inda ake ganin masu matsanancin ra'ayi a Faransa suna yada labaran kage, domin janyo tarnaki a dangantaka tsakanin kasashen musamman a fagen siyasar kasa da kasa. Sai dai za a iya cewa babu makanmancin haka daga bangaren Jamusawa. Tun dai a shekara ta 2017 ne Shugaba Emmmanuel Macron na Faransa ya nuna bukatar sabunta yarjejeniyar tsakanin kasashen na Faransa da Jamus.