1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta karrama Merkel da lambar yabo

Abdullahi Tanko Bala
April 17, 2023

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta karbi lambar yabo mafi girma ta kasa a wannan Litinin duk da sukar lamirin da ake yi na ayyukan da ta yi a zamanin mulkinta musamman manufofinta a kan Rasha.

https://p.dw.com/p/4QCbN
Deutschland Berlin | Verleihung Großkreuz des Verdienstordens an Angela Merkel durch Frank-Walter Steinmeier
Hoto: John MacDougall/AFP/Getty Images

Merkel wadda ta jagoranci kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar turai daga shekarar 2005 zuwa 2021 ta karbi lambar yabon mai daraja wanda shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier zai mika mata a wannan Litinin.

Duk da cewa ta sami karbuwa da farin jini a galibin zamanin mulkinta, Merkel mai shekaru 68 da haihuwa, farin jininta ya dusashe bayan da ta sauka daga karagar mulki a watan Disamba 2021.

Musamman shugabar wadda ta shafe shekaru 16 a karagar mulki na shan suka saboda manufar ta kan shugaban Rasha Vladimir Putin da dogaron da ta bari Jamus ta cigaba da yi da makamashin Rasha, raunin da yakin Ukraine ya bankado.