1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pistorius ya zama minisdtanb tsaro

Zainab Mohammed Abubakar
January 17, 2023

Shugaban gwamnati Olaf scholz ya tabbatar da nadin dan siyasar jam'iyyar SPD kuma ministan cikin gida na jihar Lower Saxony, Boris Pistorius a matsayin sabon ministan tsaro.

https://p.dw.com/p/4MKMS
Deutschland neuer Verteidigungsminister Boris Pistorius
Hoto: Julian Stratenschulte/dpa/picture-alliance

Scholz ya ce Pistorius shi ne mutumin da ya cancanci wannan mukami, a matsayin shi nafitaccen dan siyasa wanda ke da kwarewa a bangaren gudanrwar gwamnati, kuma ya jima cikin tsare-tsaren harkokin tsaro.

Rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr na bukatar sabon jagora da ke da sanin makamar aiki, a cewar Kansila Scholz.

Nadin sabon ministan tsaron ya biyo bayan murabus din Christine Lambrecht, a daidai lokacin da ma'aikatar tsaron kasar ke cikin wadi na tsaka-mai-wuya na matsin lambar bukatar gwamnatin Jamus  ta aike da tankunan yaki zuwa Ukraine.